Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci ta jamhuriyar muslunci ta Iran cewa, an gudanar da gasar kur’ani ta makarantun musulmi a kasar Afirka ta kudu wadda ofishin yada al’adun muslunci na Iran a kasar ya dauki nauyinta.
Am kasa gasar ne zuwa bangarori biyu, da suka hada da karatu da kuma harda, kamar yadda daga karshe kuma aka gudanar da mataki na karshe wanda aka fitar da na daya da na biyu da kuma na uku, an bayar da kyautuka na baki daya ga dukkanin wadanda suka halarci, da kuma kyautuka da aka bayar ga wadanda suka nunakwazo.