IQNA

Karatun tafsirin Kur’ani Mai Tsarki A Ghana

19:39 - June 10, 2017
Lambar Labari: 3481597
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da karatun tafsirin kur’ani mai tsarki a yankin Tamale da ke Ghana a cikin wannan wata na Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci ya habarta cewa, a cikin wata mai alfarma shekh Abdulmumin Dalahu yana gudanar da karatun tafsirin kur’ani mai tsarkia cibiyar Ahlul bait (AS) da ke yankin.

Malamin yana gabatar da karatun ne tare da halartar musulmi na yankin da suke amfana da abubuwan da yake gabatarwa a cikin wannan wata mai albarka.

Sheikh Abdulmumin baya ga tafsirin kur’ani, yana gabatar da jawabai dangane da hiimar da ke tatatre da azumin watan Ramadan mai alfarma.

3607966


captcha