IQNA

Shekaru 44 Wani Makaho Mahardaci Yana Karatun Kur’ani A Masallaci A Turkiya

19:42 - June 10, 2017
Lambar Labari: 3481598
Bangaren kasa da kasa, an kwashe shekaru 44a jere wani makaho makaranci kuma mahardacin kur’ani da shekaru 67 yana karatu a masallacin Khatunia na lardin Manisa a Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na jaridar Alqabs ta Kuwait ya bayar da rahoton cewa, Abdulmutallab Sari Kaya dan shekaru 67 an haife shi ne a garin Manisa.

An haife shi a matsayin makaho kuma ya koyi karatun kur’ani ne tun yana dan shekaru 10 da haihuwa, amma daga bisani kuma ya hardace kur’ani baki daya.

Daga bisani yay a rika yin karatun kur’ani mai tsarki a masallacin manisa a kowane watan azumin Ramadan, inda yak an karanta izihi biyu a kowace ranara, jama’a suna zaune suna sarara, ya kammala karatun kur’ani iazihi sattin a daren sallah.

Yanzu shekaru 44 kenan a jere wanan mutum da Allah yay i wa wannan babbar baiwa yana gudanar da wannan aiki.

3607924


captcha