Kame wannan malami dai ya zo a daidai lokacin masarautar kasar take ci gaba da takura ma ‘yan asalin kasar wadanda mabiya mazhabar shi’a ne, amma takan fake da dalilai na siyasa kan cewa ana nuna rashin amincewa ne da salon mylkin mulukiyya na kasar.
Tun kafin wannan lokacin dai masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta kame daruruwan malamai da fitattun ‘yan siyasa da masu fafutukar kare hakkokin bil adama a kasar, ba tare da bayyana wa duniya wani dalili na hankali kan aikata wannan danyen aiki ba.
Dukkanin bangarori na kasa da kasa da kuma majlaisar dinkin duniya gami da manyan koungoyoyin kare hakkin bil adama na duniya duk sun yi tir da Allah wadai da irin wannan mumman salon siyasa da masarautar kama karya ta kasar Bahrain ke bi wajen murkushe masu sabanin ra’ayin siyasa da ita.
Wannan kuma yana zuwa ne a daidai lokacin kasashen da ke da’awar kare hakkin bil adama da dimukradiyya irin su Amurka da ‘yan korenta daga cikin turawa irin su Birtaniya, suke mara baya ido rufe ga irin wadannan matakai na kama karya na masarautar Bahrain.