Mukhtar Juma'a ya bayyana cewa, wananns hiri yana da matukar muhimamnci ga al'ummar masar idan aka yi la'akari da irin rawar da suka takawa wajen habbaka lamurran da suka danganci kur'ani mai tsarki.
Ya ci gaba da cewa, babbar manufar kafa wannan majalisa it ace, hada malaman kur'ania wuri guda domin samun daidaito a tsakaninsu a kan dukkanin batutuwa da suak shafi kur'ani wajen daukar mataki ko zartarwa.
Dangane da wadanda za su asance mambobin majalisar kuwa ya bayyana cewa, malamai masana kur'ani da kuma da sauran masana a kan harkokin zartarwa na kasa, domin majalisar ta hada bangarorin da za su taimaka mata wajen yanke komai bisa yadda ya dace da al'umma da kuma yanayin kasa.
Ya kara da cewa hakan zai taimaka matuka wajen saukake ayyukan da suke daukar lokaci kafin yanke hukunci ko daukar mataki a kansu da suka danganci kur'ani, inda wannan majalisa za ta tattauna kuma ta dauki mataki.
A cikin makon da ya gabata ne dai ministan ya ce ba za su taba mincewa da karbar kudi a kasar ba domin koyar da kur'ani, inda y ace ma'aikatarsa ce take da hakkin biyan malaman kur'ani a kasar.