Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin almisriyun cewa, mataimakin ministan kula da harkokin adini a Masar a yankin Iskandariyya Sheikh Muhammad Alajmi ya bayyana cewa, yanzu haka wannan shiri ya yi nisa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, shirin ya kunshi gina sabbin masallatai a cikin lardin na Iskandariyya, tare mayar da su wurare na yin salla da kuma koyar da karatu da hardar kur’ani mai tsarki, inda yanzu haka ana horar da malama da limamai kusan 500 da su dauki nauyin gudana da wannan aiki.
Malamin ya ci gaba da cewa wannan shiri ba zai takaita da wadannan sabbin masalata, za a fadada shirin har zuwa wasu masallatan na daban, bisa la’akari da girman lardin da kuma bukatar mutane zuwa ga shirin.
Kamar yadda ya bayyana cewa yanzu mutane suna yin rijistar sunayensu domin shiga cikin shirin, inda kuma an dauki mutane da dama da za a fara da su.
Ya kara da cewa daga cikin abubuwan da za a mayar da hankalia akans har da koyar da wasu bangarori na addini baya ga kur’ani, kamar yadda kuma za a wayar da kan jama’a dangane da hakiaknin koyarwar kur’ani ta fuskar zaman lafiya tare da sauran addinai, da kuma kaucewa fadawa cikin akidun kafirta musulmi da ke haifar da ta’addanci da sunan addini.