IQNA

Mata Fiye Da Dubu 34 Ne Ke Samun Horon A Cibiyoyin Kur'ani Na Qatar

22:07 - July 09, 2017
Lambar Labari: 3481684
Bangaren kasa da kasa, cibiyoyin kur'ani a kasar Qatar suna horar da mata fiye da dubu 34 daga kasashen duniya daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Alarab ta kasar Qatar cewa, daga farkon wananns hekara ya zuwa yanzu cibiyoyin kur'ani na kasar ta Qatar sun dauki mata fiye da dubu 34 da suke samun horo a kan kur'ani mai tsarki.

An gudanar da wanann shiri ne tare da halartar malamai masu kwarewa abangarori daban-daban na kur'ani da yawansu ya kai dubu 9 da 115, inda suke koyar da mata mahalrta horon ilmomin daban-daban da suka shafi kur'ani.

Daga ciki kuwa akwai karatu da kuma harda, gami da wasu ilmomi da suka danganci kur'ani, kamar sanin kissoshinsa da kuma hukunce-hukuncen ayoyi, da kuma abubuwa da kur'ani mai tsarki yake koyarwa na daga kyawawan dabiu.

Babbar manufar gudanar da wannan horo dai kamar yadda hadakar cibiyoyin ta sanar shi ne, karfafa mata abangaren kur'ani da sanin abin da yake koyarwa, kasantuwar mata suna da matsayi a cikin al'umma musamman ta fuskar tarbiyantar da al'umma tun daga cikin gida, wanda hakan ke tabbatar da cewa bai kamata bar mata a baya a bangaren kur'ani da koyarwarsa.

3616714


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha