Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga
shafin yada labarai na el-massa.com cewa, Allah
ya yi wa babban malamin addinin muslunci masanin kur'ani Sheikh Allamah
Abdulkarim Al-makhlufi rasuwa a kasar Aljeriya. Shehin malamin wanda ya
tarbiyantar da daruruwan malamai a kasar Aljeriya da a halin yanzu suke bayar
da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimin kur'ani da sauran ilmomin muslunci a
kasar.
An
haife shia shekara ta 1939 a garin Adrar
na Aljeriya, Allamah Al-makhlufi ya kasnce mutum ne da aka shede shi da
kyawawan dabi'u da girmama mutane da yawan bautar Allah, baya rigima da kowa
saboda bambancin ra'ayi ko fahimta.
Ya rasu yana da shekaru 78 a
duniya, bayan kwashe mafi yawan lokutansa yana hidima ga addinin muslunci.
3617733