IQNA

Jami'an Tsaron Al Saud Sun Kashe Fararen Hula 5 A Yankin Qatif

23:40 - July 28, 2017
Lambar Labari: 3481745
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga yankunan gabashin kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa a cikin kwanaki biyu jami'an tsaron masarautar iyalan gidan saud sun kasashe fararen hula 5 a yankin Qatif ba tare da bayyani wani dalili na yin hakan ba.
Kamfanin dillancin labaran IQNa ya habarat cewa, Tashar talabijin ta almayadeen ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron masarautar ta Al Saud sun kwanha a daren jiya suna ta harbe-harben bindiga a kan gidan jama'a, inda suka jikkata mutane da dama tare da jefa mata da kananan yara cikin firgicci da tsoro.

Rahoton ya ce jami'an tsaron sun harbe wani magidanci mai sun Muhsen Al'aujami a lokacin da ya fito bakin kofar gidansa a yammacin jiya.

Haka nan kuam wasu rahotonnin sun baya ga wannan magidancin sun kara harbe wani matashi, kamar yadda akuma suka harbe mutane 3 da suke rayuwa a cikin garinsu a tsakanin danginsu ba tare da wani dalili ba.

Kungiyoyin kare-hakkin bil adama na duniya sun yi tir da Allah wadai da abin da suka kira bakin mulki na kama karya a kan fararen hula 'yan masu cikakken hakki, tare da yin kira ga majalisar dinkin duniya ta gaggauta daukar matakin takawa mahukuntan masarautar 'yan'yan gidan Saud birki kan kisan gillar da suke wa fararen hula saboda dalilai na siyasa.

3623794


captcha