IQNA

An Canja Kyallen Dakin Ka’abah

19:56 - August 31, 2017
Lambar Labari: 3481851
Bangaren kasa da kasa, a yau an canja kyallen da ke lullube da dakin Ka’abah kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin tashar alalam ya bayar da rahoton cewa, kamar yadda aka saba kowace shekara a yau an cire labulen dakin an saka sabo wanda aka dinka da zaren alhariri zalla, wanda tsawonsa ya kai ita 14 sama.

Baya ga bababn kyallen akwai wani karamin kyalle da ake sakawa wanda yake zagaye dakin baki daya daga sama, wanda fadinsa ya kai mita 47, kamar yadda tsawonsa ya kai CM95.

Kyallen dakin Ka’abah bisa ga alada dai ana canja ne a kowace ranar 9 ga watan zulhijja, wato ranar tsayuwar Aarafah, wanda aka cire kuma ana ajiye shi a cikin wani daki na musamman.

3636717


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha