IQNA

ISESCO Ta Bukaci A Kwace Lambar Nobel Da Aka Bai Wa Suu Kyi

17:13 - September 05, 2017
Lambar Labari: 3481866
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ISESCO ta bukaci da a gaggauta kwace lambar yabo da aka baiwa Suu kyi ta Nobel ba tare da wani ba ta lokaci ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na freepen ya bayar da rahoton cewa, kungiyar ta ISESCO ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar daga babban ofishinta da ke birnin Rabat na kasar Morocco.

A cikin bayanin kungiyar ta bayyana cewa, mutanen irin su Aung San Suu Kyi ba su cancanci samun lambar yabo ta zaman lafiya ta nobel ba, idan aka dubi irin kisan kiyashin da gwamnatinta take yi wa musulmi a kasar Myanmar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, kisan kiyashin da ake yi wa musulmi a halin yanzu haka akasar Myanmar, lamari ne da ya cancanci dukkanin kasashen duniya su dauki matakin ladabtarwa a kan gwanatin kasar Myanmar a kansa, sakamakon kisan dubban muusulmi 'yan kabilar Rohingya a cikin kasa da mako guda.

Haka nan kuma bayanin ya bukaci da a gurfanar da Aung San Suu Kyi a gaban kotun manyan laifuka ta duniya domin ta fuskanci hukunci.

3638682


captcha