IQNA

An Bude Taron Zaman Majalisar Dokokin Holland Da Karatun Kur’ani

23:47 - September 21, 2017
Lambar Labari: 3481919
Bangaren kasa da kasa, an bude zaman majalisar dokokin kasar Holland da karatun kur’ani mai tsarki a cikin babbar majami’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Zaman cewa, an bude tarn ne tare da halartar ‘yan majalisa da kuma firayi ministan kasar Mark Tory.

Ayar da aka karanta a wurin ita ce ayar da ke cewa daga Allah muke kuma zuwa ga Allah za mu koma.

Wannan aya tana dauke da abubuwa da dama da take yin ishara da su da kuma koyar da dukkanin ‘yan adam, daga ciki kuwa har nuni dukkanin halittu mutane da aljannu da kowa duk daga Allah suke, kuma halittarsu da rayuwarsu ba karshenta duniya b ace.

Ayar na nuni da cewa dukkanin talikai za su koma zuwa ga Allah madaukkakin sarki mahaliccinsu.

Wannan taro ya samu halartar dukkanin bangarori da suke majalisar ta kasar Holland da suka hada da kiristoci da yaudawa da kuma musulmi gai da ‘yan buda.

Kasar Holland daga cikin kasashen turai da ke bayar da dama ga dukkanin addinai da mabiyansu su rayu a kasar, duk kuwa da bullar kungiyoyi masu akidar kin musulmi.

3644731


captcha