Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, A yau alhamis ne ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke gabacin Asiya, ya
fitar da sanarwa da ta kunshi cewa a karon farko masu bincike na majalisar sun
sami izinin gwamnatin kasar Myanmar domin shiga kasar da kuma isa
yankin Rakhine na tsirarun musulmin kasar.
Gwamnatin kasar ta Myanmar ta bada izinin shiga yankin na Musulmi ne adaidai lokacin da kwamitin tsaron Majalsiar Dinkin Duniya ya yi zama na musamman akan lamarin.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniyaya ce masu binciken za su shiga cikin kasar ta Mayanmar bisa aiki tare da gwamnatin kasar.
Har ila yau ya ce; Shugabannin hukumomi daban-daban da su ke karkashin Majalisar Dinkin Duniyar za su kasance a tare da masu binciken.