Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sharq al'ausat cewa, a daidai lokacin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah suke gudanar da tarukan tunawa da Ashura, jami'an tsaron gwamnatin Masar na takura musu.
Bayanin ya ci gaba da cewa, mahukuntan kasar ta Masar sun dauki matakin rufe kofofin masallacin Ra'asul Hussain (AS) da ke birnin Alkahira.
Wannan mataki dai ba shi ne na farko ba, domin kuwa tun bayan da shugaban Masar mai mulki a yanzu ya yi juyin mulki, ya dauki matakai da dama masu ban mamaki dangane da mabiya mazhabar shi'a a kasar.
Daga cikin matakan kuwa har da takura musu da hana su gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba yi a tsawon tarihi, kasantuwar kasar Masar kasa ce wadda take da masaniya kan mazhabar ahlul bait tun tsawon tarihin muslunci.
Dukkanin gwamnatocin baya-bayan na da aka yi a kasar Masar har da gwamnatin Mubarak ba su taba hana mabiya mazhabar ahlul bait gudanar da harokinsu ba, domin kuwa suma 'yan kasa ne da suke da hakki a kasarsu kamar kowane dan kasa.
Bayan da aka kifar da gwamnatin Mubarak an fara samun matsala a kasara lokacin da masu ra'ayin muslunci da suke dauke da akidar salafiyanci da wahabiyanci suka rike madafun iko a karkashin shugabancin morsi wanda aka yi wa juyin mulki daga bisani.
Yanzu haka dai gwamnatin Masar mai ci duk kuwa da cewa babu ruwanta da addini, amma saboda tasirin kasashen da suke bata kudade masu yada akidar wahabiyanci, hakan ya sanya ta daukar matakai na neman hana mabiya mazhabar ahlul bait gudanar da harkokinsu, duk kuwa da cewa bas u taba zama barazana ga wani dan kasa ba, kamar yadda sauran addiniai da akidu a kasar suke komai nasu a cikin 'yanci haka suke da hakki, amma kuma an haramta musu yin hakan.