Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daruruwan mabiya addinai na kiristanci da muslunci da kuma yahudawa sun gudanar da wani tattaki na bai daya a birnin Devis na jahar California domin samar da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai.
A yayin tattakin wanda aka fara daga wata majami’ar yahuwa, musulmi da kiristoci da kuma yahudawa sun hadu wurin guda, inda suka shiga cikin tare suna gaisawa da sauran jama’a.
Wannan lamari ya burge jama’a da dama, ganin yadda shugabannin dukkanin wadannan manyan addinai suka hadu wuri guda a cikin zaman lafiya da fahimtar juna.
Akwai da dama daga cikin kirostoci da yahudawa a kasar Amurka da suke nuna rashin jin addinsu kan yadda ake gallazawa musli tare da nuna musu kyama kasar, musaman bayan zuwa wannan sabuwar gwamnatin ta Amurka.
Wannan mataki dai ya zo ma mutane da dama da ban mamaki da kuma ban sha’awa, domin ta haka ne al’umomi za su fahimci juna kuma su zauna lafiya ba tare da wani ya shiga hakkin wani ba, yayin da kowa yake yin addininsa daidai fahimtarsa.