Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Alsharq cewa, an bude baje kolin fasahar rubutun muslnci mai taken addinin muslunci addinin zaman lafiya da sulhu a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar.
Ana gudanar da wannan baje koli ne bisa kulawar babban dakin karatu na birnin Iskandariya birnin na biyu mafi girma a kasar, inda aka baje kolin alluna da kuma ababen da aka yi rubutun muslunci ta hanyoyin na fasaha.
Jaudat Muhammad ya ce akwai masu fasahar rubutun muslunci su 50 daga kasashen duniya da suka hada da nahiyar turai da kuma Afirka gami da Indonesia da Iraki duk suna halartar wurin, kuma sun kawo ababen da suka yin a fito da wannan take.
Taron dai ya samu karbuwa daga jama’a da dama da suke zuwa wurin domin duba irin abubuwan da aka ajiye domin jama’a masu zuwa dubuwa, daga cikin masu halartar wurin kuwa har da wadanda ba muslmi da suka hada da yan yawan shatawa da bude ido.