Wannan masalalci dai kwamitin musulmi jamus 'yan asalin Turkiya ne suka gina shi, kuma wannan kwamiti nasu ya gina masallatai fiye da 900 a fadin kasar ta Jamus.
Hukumar da ke sanya ido kan harkokin zamantakewar jama'a a kasar Jamus SETA ta sanar da cewa, kyamar musulmi na karuwa matuka akasar a cikin lokutan baya-bayan nan, inda hare-haren suka ninka daga shekara ta 2015 ya zuwa har sau hudu.
Masu kyamar musulunci a kasar Jamus dai suna yin barazana ne ga masallatai da kuma cibiyoyin msulunci da suke cikin yankuna daban-daban na kasar.