Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan gasa za a gudanar da ita ne tare da hadin gwaiwa da ma’aikatar magajin gari ta lardin Gabiri a Lebanon.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa za a gudanar da ita a bangarori biyu na mata da maza, inda za ta kunshi bangarori uku da za a kara a kansu, wato tilawa da kuma harda gami da tafsiri.
Tiwar za ta kunshi tajwidi da kuma karatun tartili, sai harda juzui 30 da juzui 20, sai kuma juzui 10 da kuma juzui 5, yayin da tafsirin zai kama daga shafi na 96 zuwa na 166 cikin littafin tafsir na Almizan.
Za a raba wurin gudanar da gasar zuwa Ba’alabak da Hirmil, sai kuma Beirut da Sur gami da Nabdiyya. Wannan gasa dai tana daga cikin muhimamn gasar kur’ani da ake gudanarwa akasar ta Lebanon wadda cibiyar Taujih wal Irshad da ke karkashin kungiyar Hizbullah ke daukar nauyinta.