IQNA

Taron Masana Na Kasa Da Kasa A Masar Ya Yi Tir Da Duk Wani Aikin Ta’addanci

21:16 - October 29, 2017
Lambar Labari: 3482050
Bangaren kasa da kasa, taron masana musulmi na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Gardaqah na Masar ya yi tir da Allah wadai da duk nauin ayyukan ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yaum sabi cewa, an kamma taron masana musulmi na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Gardaqah na Masar wanda ya yi tir da Allah wadai da duk wani aikin ta’addanci a duniya.

Wannan taro ya samu halartar masana 150 daga ciki da wajen kasar ta Masar, da suka hada da wakilan kasha 18 na larabawa da wadanda ban a larabawa ba.

Mahalrta taron wadanda mafi yawansu fitattun malaman jami’oi ne da marubuta, sun mayar da hankali ne a makalolin da suka rubuta a kuma suka gabatar a wurin taron, kan manyan matsaloli da kalu bale da ke fuskantar duniyar muslmi a halin yanzu.

Masanan suna ganin cewa akidar wahabiyanci wadda ta bullo a cikin al’ummar musulmi ita babbar fitina wadda ta tarwatsa kan musulmi da suke zaune da juna lafiya duk da sabanin fahimta kan wasu lamurra, inda akidar wahabiyanci take azuzu duk wani sabanin fahimta da kuma raba kan msuulmi.

Baya ga haka babban abin da yafi muni shi ne haifar da akidun ta’addanci da sunan muslunci da akidar wahabiyanci take yi tare da kasha makudan kudaden man fetur, kasantuwar kasashen da wahabiyawa suke rike da madafun iko suna da arzikin man fetur wanda ake amfani da hakan domin yada wannana kida, inda taron ya yi kan a dauki matakin tunkarar wannan lamari.

3657983

captcha