Bayanin ya ci gaba da cewa wannan hanya an jima an amafani da ita a yankuna da dama da suke kusa da tekun bahr ahmar musamman wadanda suke cikin kasar Masar.
Baya ga haka kuma akwai wasu daga cikin kasashen larabawan yankin arewacin afrika da suke yin amfani da wannan hanya ta karatun allo tsawon daruruwan shekaru, wanda ta hanyar haka ne lamarin ya isa ga kasashen yammacin afrika.
Yanzu haka dai wannan salo ya zama daya daga cikin al'adu da wasu gwamnatoci suka yi kokarin kawo karshensu Masar da wasu kasashen yankin, amma abin ya faskara, domin kuwa ya zama hanya ta koyon karatu da aka gada kamar yadda haka lamarin yake a yammacin afrika.