IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Musulunci A Canada

23:44 - November 02, 2017
Lambar Labari: 3482060
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman tar na karawa juna sani kan mslunci a birnin Saskatoon da ke jahar Saskatchewan a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na global news cewa, a jiya aka fara gudanar da taron, wanda ya kunshi shirye-shirye daban-daban.

Ana gudanar da taron ne a ginin babbar cibiyar muslunci da ke birnin, kuma ana samun halartar mabiya addinai daban-daban gami da muuslmi, inda ae gabatar da jawabai kan addinin muslunci da kuma amsa tambayoyi daga bangaren mahalarta taron, musamman ma wadnda ba musulmi ba.

Kasar Canada tana daga cikin kasashen da musumi suke fuskantar matsaloli na zamantakewa tare da jama’a, kasantuwar mafi yawan al’ummar kasar mabiya addinin kirista ne da basu da masaniya kan addinin musulunci.

Farfagandar da wasu masu kiyayya da musulmi suka yi ta yi tasiri a kan wasu mutaen kasar, inda halin yanz har a kan samu masu kai hari kan masalatai da cibiyoyin msuulmi, abin da ba a saba ganin irinsa akasar ba.

3659429


captcha