IQNA

Littafin "Mace Da Musulunci" Ya Lashe Gasar Atlas A Morocco

21:20 - November 05, 2017
Lambar Labari: 3482068
Bangaren kasa da kasa, littafin mace da muslucni na Asma Murabit wata likita kuma marubuciya 'yar kasar Morocco ya lashe gasar Atlas.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na kifache.com cewa, Asma Murabit ta rubuta wannan littafi ne domin yin bayani kan matsayin mace a mahangar mulsunci ta fuskoki daban-daban.

Daga cikin abin da tafi mayar da hankali a kansa akwai matsayin mace ta fuskar rayuwar zamantakewa, da kuma irin gudunmawar da za ta iya bayarwa wajen ci gaban al'umma da tarbiyarta.

A kowane lookaci muslucni yana kare hakkokin mutum ne tare da nema masa 'yancinsa na rayuwa, domin ya fita daga bautar abin halitta zuwa ga bautar mahaliccinsa, wanda hakan shi ne hakikanin 'yanci.

Littafin ya yi ishara da cewa, mata suna da rawar da za su taka a bangarori daban-daban na rayuwar al'umma, bil ahasali akwai bangarori wadanda mata ne kawai za su ya taka rawa a cikinsu.

Daga ciki akwai tafiyar da iyali daga cikin gida da kula da su da tarbiyarsu, wanda muslunci ya tsara abubuwa da dama da mace za ta dauka domin gudanar da wannan gagarumin aiki, wanda bai gaza aikin maza ba na neman abin rayuwa.

Wannan littafi ya samu wannan kyauta ne daga babbar cibiyar yada a'adu ta Faransa da kuma Morocco.

3660194


captcha