Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto da shafin Almzab cewa, gunguma masana da lauyoyi da kuma ‘yan jarida har da ‘yan siyasa daga kasashe daban-daban ne suka zo Karbala a wanann shekara tare da shiga tattaki domin ganewa idanunsu yadda wannan taron jama’a mafi girma a duniya yake gudana.
Kasashen sun hada da Amurka, Canada, Rasha, Argentina, Bolivia, Lebanon, Brazil, Uruguay da sauransu, kamar yadda wasu da dama daga kasashen Afrika da na asia duk sun samu halartar wannan taro.
Wadannan masana sun bayyana cewa babban abin da ya kawo su shi ne, ganwa idanuns abin da ake yi, domin kuwa tara mutane miiyo da sukan haura miyan ashirina wuri guda, ya tabbatar da cewa lallai lamari ne mai girma.