IQNA

Karbala Ta Dauki Nauyin Taron Addini Mafi Girma A Duniya

22:20 - November 10, 2017
Lambar Labari: 3482084
Bangaren kasa da kasa, birnin Karbala mai alfarma ya dauki nauyin taron addini na ziyarar arbaeen na Imam Hussain (AS) wanda shi ne taro mafi gima a duniya ta fuskar mahalarta.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, Rahotanni daga kasar Iraki na nuni da cewa miliyoyin mabiya da masoya Ahlulbaiti (a.s) daga duk fadin duniya suna ci gaba da taruwa a birnin Karbala na kasar Irakin don gudanar da juyayin Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da cikar kwanaki arbaeen da kisan gillan da aka yi wa Imam Husainin da iyalai da magoya bayansa a shekara ta sittin da daya bayan hijirar Ma'aiki (s).

Rahotannin sun ce tun jiya ne dai miliyoyin mutanen suke ta isowa birnin na Karbala mafi yawansu suna tattaki daga birnin Najaf da ke kimanin kilomita sabain da shida daga birnin Karbala din don halarta taron na Arba'in da ake ci gaba da gudanar da shi a yau din nan Juma'a.

Rahotanni daga Irakin sun ce gwamnatin kasar ta dau tsauraran matakan tsaro a garin Karbala din da kewayensa da kuma dukkanin hanyoyin shigowa garin don kiyaye lafiyar masu ziyarar daga duk wata barazana da za ta iya samun lafiyarsu.

Taron juyayin ranar Arba'in din dai ana gudanar da shi ne a ranar ashirin ga watan Safar na kowace shekara, wato kwanaki arbain bayan kisan gillan da aka yi wa Zuriyar Annabi a Karbala din a ranar goma ga watan Muharram na shekara sittin da daya.

3661724


captcha