IQNA

22:23 - November 10, 2017
Lambar Labari: 3482085

An Kammala Shirin Ayyukan Kur’ani Na Arbaeen

Bangaren kasa da kasa, an kammala shirin ayyukan kur’ani da aka gudanar a lokacin tattakin arbaeen a ckin larduna daban-daban na kasar raki.

An Kammala Shirin Ayyukan Kur’ani Na Arbaeen

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na qaf ya habarta cewa, an kawo karshen shirin ayyukan kur’ani da aka gudanar a lokacin tattakin arbaeen a ckin larduna daban-daban na kasar Iraki a kan hanyar zuwa birnin karbala mai alfarma.

Muhammad Khalil shi ne babban darakta na shirin kur’ani da ae gudanarwa akan hanyar Karbala a lokacin tarukan zyarar arbaeen, ya bayyana cewa a cikin yardarm Allah wannan shiri y gudana a cikin nasara.

Ya ce fiye da malaman kur’ani dubu ne suka bayar da gudunmawa wajen jagorantar shirin, a kuma kafa wurare 450 a cikin larduna 13 na Iraki a kan hanyar zuwa Karbala.

Daga cikin ayyukan da aka gudanar akwai zaman karatun kur’ani da kyautata tilawa, da kuma koyar da hukunce-hukuncen karatun kur’ani, sai kuma fitar da darussa da suke a cikin ayoyin kur’ani mai tsarki, tare da tafsirin ayoyi.

Abin tuni a nan dai shi ne, wannan shiri ana gudanar da shi tsawon shekaru uku a jere, tare da halartar miliyoyin masu zyara da suke yada zango a wadannan wurare.

3661727


captcha