IQNA

23:35 - November 11, 2017
Lambar Labari: 3482090

Wata Jaridar Najeriya Ta Yi Rubutu Kan Taron Arbaeen

Bangaren kasa da kasa, wata jaridar Najeriya People's Daily ta rubuta rahoto a kan taron Arbaeen da aka gudanar a Karbal.

Wata Jaridar Najeriya Ta Yi Rubutu Kan Taron Arbaeen

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada al'adun musulunci cewa, jaridar Peoples Daily da ake bugawa a Najeriya ta rubuta rahoto a kan taron Arbaeen da aka gudanar a Karbala na kasar Iraki.

Jaridar ta ce wannan taron shi ne taron addini mafi girma da ake gudanarwa a duniya, wanda miliyoyin musulmi mabiya mazhabar shi'ar ahlul bait (AS) suke gudanarwa a kasar Iraki.

Wannan taron ya samo asali ne tun bayan waki'ar Ashura, inda aka kasha Imam Hussain (AS) tare da zuriyar manzon Allah da suke tare a Karbala, inda ake tunawa da abin da ya faru da kuma yin alhini kan hakan.

Tun bayan lokacin da Saddam Hussain ya kwace iko a kasar Iraki, ya hana gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da zaluncin da aka yi wa iyalan manzon Allah a bayansa, amma bayan kawar da shi daga mulki, an ci gaba da gudanar da tarukan.

3662129


captcha