Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada
labarai an Netral News ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne aka farafara zaman
taro da reshen jamiar Azhara kasar
Indonesia ya shirya na kara wa juna sani kan muhimamn hanyoyin bunkasa ci gaban
addinin muslunci a zamanance.
Asep Saifuddin shi ne shugaban jami'ar reshen Azhar da ke kasar Indonesia, ya bayyana cewa babbar manufar shirya zaman taron dai ita ce, fitar da sabbin hanyoyi na bunkasa karantarwar addinin muslunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Indonesia na daga cikin kasashen musulmi da a halin yanzu suke samun ci gaba cikin sauria dukkanin bangarori na yada addinin muslunci da koyarwarsa.
Da dama daga cikin wadanda suka halrci taron sun bayyana wajbcin yin amfani da hanyoyi na ilmantarwa da zasu dakushe yunkurin wasu masu yada akidar ta'addanci da sunan muslunci da suke kafirta musulmi suna kiransu mushrikai ko 'yan bidi'a.