Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, 'yan mintunan da suka gabata ne aka bude babban taron makon hadin kan al'ummar msuulmi a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran tare da malamai da masana da masana a babban dakin taruka na birnin.
Wannan taro wanda shi ne karo na talatin da daya da ake gudanar da shi, yana samun halartar baki kimanin 500 daga sassa na duniya, da nufin kara karfafa hadin kan al'ummar musulmi da kuma tabbatar da cewa musulmi sun zama cikin fadaka a kan halin da aka jefa su a ciki.
An kafa kwamitoci guda 6 wadanda za su gudanar da zama tare da tabbatar da cewa an bi diddigin dukkanin abubuwan da aka cimmawa, daga cikin kwamitocin akwi kwamitin hadin kan musulmi da kuma ci gaban al'ummar musulmi a zaman yau, haka nan kuma akwai kwamitin bunkasa al'adun musulunci da rarrabewa tsakaninsu da al'adun yammacin turai, sai kuma kwamitin ayyukan alkhairi, haka nan kuma za a kafa wasu kwamitocin na daban da suka shafi gwagwarmayar malaman musulunci.