IQNA

Shugaba Rohani A Wajen Taron OIC:
23:16 - December 13, 2017
Lambar Labari: 3482198
Bangaren kasa da kasa, Shugaban Jamhriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya gabatarwa duniyar musulmi shawarwari guda bakwai domin kalubalantar kudurin shugaba Trump na Amurka a game da birnin Qudus, inda ya ce Amurka tana kare manufofin sahayuna ne ba tare da yin la'akari da na al'ummar Palastinu ba.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habata cewa: A yayin da ya gabatar da jawabinsa a taron gaggawa na shugabannin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da ya gudana wannan laraba a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya gabatar da shawarwari  kamar haka:

Bayan sallama ga shugaba Erdogan na Turkiya mai masaukin baki.

Da kuma sallama ga dukkanin shugabannin kasashe.

Da kuma sauran baki mahalarta

Ya fara da Sunan Allah Mai Rahma Mai jin kai

A cikin shawarwarin nasa:

1 – Ya bukaci ya g taron yayi alawadai da kudirin Amurka na bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin HK Isra'ila, a matsayin shawara ta farko.

2 - Sai shawara ta biyu, inda shugaba Rauhani ya bukaci dukkanin kasashen musulmi su hade wure guda domin kalubalantar wannan matsayi da Amurka ta dauka game da birnin Qudus.

3 - Shugaban Rauhani ya ce wajibi Amurka ta san cewa Duniyar musulinci ba za tayi wasa da makomar al'ummar Palastinu da Qudus ba, kuma ta san cewa izgilanci da tayi a game kudirin kasa da kasa kan  Palastinu,dole ne ta fuskanci martani mai karfi a siyasance.

4 – Ya kamata kasashen musulmi su tsaya tsayin daka wajen kalubalantar wannan kuduri ta hanyar tattaunawa da kawayen Amurka musaman kasashen Turai domin tilasta mata ta dawo daga wannan mataki.

5 – Shawara ta biyar kuma shugaban  ya ce kamata yayi Duniyar musulimi ta sanya matsalar Palastinu a matsayin matsalar duniya ta farko da ya kamata a magance, bayan karya lagon 'yan ta'addar Da'esh a kasashenn siriya da Iraki.

6 - A matsayin shawara ta, shugaba Rauhani ya bukaci wakilan kasashen musulmi a zauren MDD da kwamitin tsaron MDD su hade wuri guda wajen kara kaimi na matsin lamba domin ganin an magance wannan matsala da kuma tilastawa Amurka na ta janye wannan kuskure da tayi, domin a halin da ake cikin zauren MDD da kwamitin tsaro gami da kungiyoyin kasa da kasa su ne za su taka mahimiyar rawa wajen bayyanawa Amurka adawarsu da wannan mataki da ta dauka a game da Qudus kuma ta janye shi cikin gaggawa.

7 – Ya kamata a kafa wani kwamiti na zama wanda zai rika bin kadun halin da ake tsakanin kasashen musulmi, wanda zai rika yin zama ko dai an shugabannin kasashe kokuma ministoci domin ci gaba da bibiyar lamarin.

A karshe Shugaba Rauhani ya ce Iran a shirye take ta hada kai da dukkanin kasashen musulmi da kuma bayar da dukkanin taimakon da ya dace domin kare birnin Qudus, sannan ya tabbatar da cewa musulmi da larabawa ba makiyan yahudawa ba ne, saidai suna adawa da shirin sahayuna mai cike da hadari ne.

3672477

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: