IQNA

Muhammad Jawad Zarif:

Za Mu Kai Karar Amurka Kan Zargin Kage Da Ta Yi Kan Iran

23:48 - December 20, 2017
Lambar Labari: 3482218
Bangaren siyasa, ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif y ace za su kai karar amurka a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan zargin Iran da ta yin a bayar da makamai.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, Ministan harakokin wajen Iran ya tabbatar da cewa Jamhuriyar musulinci ta Iran za ta shigar da karar Amurka a gaban Majalisar dinkin Duniya kan da'awar da wakiliyar Amurka a MDD ta yi na cewa Iran din na bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai.

A cikin wani sako da ya turawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa, a safiyar wannan Lahadi Ministan harakokin wajen Jamhuriyar musulinci ta Iran Muhamad Jawad Zarif ya ce kasar sa za ta shigar da karar Amurka a gaban zauren MDD game da zargin da Amurkan ta yiwa Iran na cewa ita ce ta bawa dakarun kungiyar Ansarullah na kasar Yemen makaman da suka halba zuwa filin jirgin saman birnin Riyad na Saudiya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce wakiliyar Amurka a MDD Nikki Haley ta gabatar da wasu gututturan karafuna tare da da'awar cewa makami mai lizzamin kasar Iran ne da ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen suka harba zuwa cikin kasar Saudiya.

Saidai kafin hakan, Mai magana da yawun MDD, Farhan Haq ya yi watsi da wannan zargi.

3674661

 

 

captcha