IQNA

An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan 'Yan Ta'adda 15 A Masar

16:44 - December 27, 2017
Lambar Labari: 3482242
Bangaren kasa da kasa, Mahukutan kasar Masar sun sanar da cewa an zartar da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa kan wasu mutane 15 saboda samunsu da hannu cikin ayyukan ta'addanci musamman a yankin Sina'i na kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jami'an kasar Masar din suna cewa a jiyar Talata ce aka zartar da wannan hukuncin kan wadannan mutane da aka yanke wa hukumcin kisa din a wani lokaci a baya bayan da aka same su da laifin kai hare-haren ta'addanci kan sojoji da 'yan sandan kasar a yankin Sinai.

Rahotannin sun ce an zartar da hukuncin kisa din ne a kan mutanen a wasu gidajen yari guda biyu na kasar sannan kuma akwai wasu dubban da suke jiran zartar musu da irin wannan hukuncin.

Kasar Masar din dai tana fuskantar matsalar tsaro da hare-haren ta'addanci a kasar cikin 'yan shekarun nan tun bayan guguwar sauyi da ta kada a kasashen larabawa da ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatin shugaban mulkin kama-karya na kasar Hosni Mubarak da kuma gwamnatin 'yan Ikhwan karkashin jagorancin hambararren shugaban kasar.

3676596

 

 

captcha