Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Russia Today cewa, bisa ga al’ada a kowace sabuwar shekara ana gayyatar shugabannin mabiya addinai a taron addu’ar sabuwar shekara wanda ake gudanarwa a fadar shugaban kasa da ke birnin Paris.
A karon farko cikin shekaru 25 a jiya an gudanar da irin wannan taro ba tare da an gayyaci babban daraktan masallacin Paris ba, wanda shi ne yake a matsayin wakilin musulmi a dukkanin lamurra da suka shafi gwamnati.
Masallacin Paris ya fitar da sanarwa da ke cewa, sakamakon rashin gayyatar Dalil Abubakar a wajen taron addu’a sabuwar shekara, kwamitin masallacin ya yanke shawar dakatar da halartar tarukan kwamitin addinai na kasar Faransa, kamar yadda kuma zai dakatar da halartar duk wasu taruka na gwamnatin kasa har sai abin da hali ya yi.