IQNA

Baje Kolin Rubtun Fasahar Muslunci A Kasar Oman

23:43 - January 07, 2018
Lambar Labari: 3482277
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje koli na kayan fasahar muslunci na wata ba’iraniya Najis Haidari a birnin Masqat na Oman.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na ciyar yada al’adun muslunci ya habarta cewa, a wajen taron baje koli da aka bude a kasar Oman Iraniyawa mazauna kasar sun bayar da gudunmawa wajen ganin yagudana a cikin nasara, inda Narjis Haidari ta gabatar da manyan alluna guda 45 masu dauke da rubutun fasar musulunci.

Wannan baje kolin dai an fara shi ne tun daga farkon wannan shekara kuma zai ci gaba da gudana har tswon kwanai 10.

Wannan shi ne karon farko a cikin wannan shekara ta 2018 da wannan mata mai fasahar rubutu ta fara gudanar da baje koli na irin abubuwan da tae samarwa.

Baya ga halarta masana da kuma jami’ai a wannan baje koli na Narjis Haidari, Hojjatol Islam Nuri Shahrudi jakadan Iran da kuma Bahman Akbari shugaban ofishin kula da harkokin al’adu duk sun halarci wurin.

3679965

 

captcha