IQNA

Taron Musulmi Kan Kafofin yada Labarai A Najeriya

16:50 - January 08, 2018
Lambar Labari: 3482278
Bnagaren kasa da kasa, wasu kungiyoyin musulmi sun shirya wani zaman taro domin yin bita kan lamurran ad suka shafi harkokin larabarai da suka shafi musulmi a Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan taro ya gudana ne a birnin Lagos babbar cibiyar kasuwanci ta tarayyar Najeriya, tare da halartar masana da kuma kungiyoyin kare hakkin musulmi.

Alhaji Laila Tala wani fitaccen dan jarida ne musulmi a Najeriya wanda ya gabatar da kasida a wajen taron, inda yake bayyana cewa hakika musulmi suna fuskantar rashin adalci daga wasu bangarori na sadarwa a kasar.

Inda ya bayyana cewa lamurra da dama suna wakana da musulmi a dukkanin yankuna na kasar, amma ba kasafai a kan bayar da rahoton yadda yake ba.

Ya ce musulmi babban bangare mai matukar muhimmanci a Najeriya, wanda dole ne a tafi da su,a  kan haka yin adalci ga musulmia  cikin dukkanin lamurra da suka shafe ko suka shafi addininsu wajibi ne.

Akintola shi ne shugaban kuniyar kare hakkin musulmi a  Najeriya, ya gabatar da tasa kasidar, inda yake bayyana muhimamncin samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin musulmi da dukkanin bangarori a Najeriya.

Tarayyar Najeriya dai tana da mutane da suka kai miliyan 180 da suka hada da musulmi da kirista.

3679746

 

 

captcha