IQNA

Kabilar Rohingya Na Tsoron Komawa Kasarsu

23:41 - January 26, 2018
Lambar Labari: 3482338
Bangaren lasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta duniya ta bayyan acewa, dubban daruruwan ‘yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira sun atsoron komawa kasarsu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran arakan ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani rahoto da ta fitar kungiyar kasashen musulmi ta duniya ta bayyan acewa, dubban daruruwan ‘yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira sun atsoron komawa kasarsu saboda kisan gillar da aka yi musu.

Rahoton yace hakika akwai babban tashin hankali dangane da abin da ya samu muuslmi ‘yan kabilar Rohingya  akasar Myanmar, inda aka yi musu kisan kiyashi tare da kona kaddarorinsu da muhlalnsu, da kuma yi ma matansu fyade.

A kwanakin baya ne gwamnatin kasar Bangaladesh ta sanar da cewa ta cimma matsaya tare da mahukuntan kasar Mayanmar kan komawar dubban darurun musulmi ‘yan kabilar Rohingya da suka tsere suka yi gudun hijira.

Sai rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawansu basu buktar komawa kasar ta Myanmar, sakamakon abin da suka ganewa idansu na kisan gilla da ‘yan addinin buda tare da sojojin kasar suka yi a kansu da iyalansu.

Manyan kasashen turai sun gum da bakunansu kamar yadda wasu daga cikin manyan kasashen larabawa suma suka nuna halin ko in kulak an halin da musulmin Rohingya suka samu kansu a hannun gwamnatin Myanmar.

3685439

 

 

 

captcha