IQNA

Gobara Ta Tashi A Birnin Makka Mai Afarma

23:53 - January 29, 2018
Lambar Labari: 3482347
Bangaren kasa da kasa, ‘yan kwana-kwana sun samu nararar shawo akn wata gbara da ta tashi a kusa da haramin Makka mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a jiya ‘yan kwana-kwana sun samu nararar shawo akn wata gbara da ta tashi a  kusa da haramin Makka mai alfarma ba tare da samun asarar rayuka ba.

Babban jami’i mai kula da harkokin agaji na birnin Makka ya bayyana cewa, gobarar ta tashi nea  was gidaje 15 da suke a kusa da harami ma tsarki, wadanda ae afani da su a matsayin ofisoshin da ake gudanar da ayyuka.

Ya kara da cewa jami’an hukumar kasha gobara sun yi kokari matuka wajen ganin sun shawo kan wannan gobara, kuma babu wani mutum da ya rasa ransa, sai an samu hasarar kayan aiki da kaddarori.

Jami’in bai yi Karin aske kan irin hasarorin da aka samu ba na kayayyaki da kuma kimarsu ba.

3686310

 

 

captcha