IQNA

Wata Mata Ta Mayar Da Mutanen Kauyensu Musulmi A Habasha

22:27 - February 08, 2018
Lambar Labari: 3482378
Bangaren kasa da kasa, Halimi Gobo Sora wata mata ce da ta mayar da mutanen kauyensu musulmi a kasar Habasha.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wannan mata ta mayar da sunanta Rabi’a bayan da ta musulunta, kuma tana da yara 5 tana zaune a kauyen Simo a kasar ta Ethiopia.

Bayanin ya ci gaba da cewa halimi ta kasa gamsuwa da addinin kiristanci da kuma abin da ake koyar da su, wannan ne ya sanya ta yi bincike kan muslunci.

Bayan da ta karbi addinin muslunci ta shiga yin bayani domin isar da shi ga sauran mutanen kauyen, kuma sun gamsu da irin bayanin da take yi musu, wannan ya sanya da dama daga cikinsu sun karbi addinin muslunci.

Ta ci gaba da cewa, wadanda suke zuwa yankin nasu domin yi musu bayani kan addinin kirista mutane wadanda basu da kyawawan halaye, sabanin musulmi da suke gani wadanda mutane ne na gari.

Kasantuwar musulmi da suke gani kuma suke mu’amala da su mutanen kirki ne hakan yayi mata tasiri har ta nemi sanin addinin muslunci da kuma koyarwarsa, bayan samun bayani kan musulunci ta gamsu da koyrwarsa.

Haka nan kuma bayanin da take yi wa sauran kiristoci mazauna kauyensu sun gamsu da shi, kasantuwar musullunci yan kira ne zuwa ga kyawawan dabiu da adalci da barin zalunci da duk wani abu da bashi da kyau a hankalce.

3689673

 

captcha