IQNA

23:15 - February 14, 2018
Lambar Labari: 3482395

Zaman Gaggawa A Kwamitin Tsaro Kan Halin Da Ae Ciki A Gaza

Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zama a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan halin da ae yanin Zirin Gaza.

Zaman Gaggawa A Kwamitin Tsaro Kan Halin Da Ae Ciki A Gaza

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Safa cewa, an gudanar da wani zama a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan halin da ae yanin Zirin Gaza bisa neman da kasashen Bolivia da Kuwait suka yi.

A zaman dai an yi dubi ne a kan irin mawuyacn halin da al’ummar Gaza ske ciki, sakamakon killace yankin da haramtacciyar kasar Ira’ila take, tare da hana shiga da magunguna da kayan abinci gami da makamashi a yankin.

Yazu haka babar matsalar da ake fuskanta wadda ta yi tasiria  dukanin harkoki ita ce rashin wuta da kuma ruwan sha, da kuma karancin magunguna a asibitoci, yayin ga gwamnatin Masar kuma daga bangarenta take ci gaba da rufe mashigar rafah.

Haramtacciyar kasar sra’ila ta dauki wannan matain n tare da cikakken goyon bayan Amurka da wasu daga cikin sarakunan kasashen larabawa, wadanda suke yin biyayya ido rufe ga Amurka da kuma yahudawa.

3691555

 

 

 

captcha