IQNA

22:51 - March 19, 2018
Lambar Labari: 3482490

An Nuna Fim Din Batunci Ga Musulunci Tashar Talabijin Din gwamnatin Holland

Bangaren kasa da kasa, an nuna fin din nuna kyama da batunci ga addinin muslunci a gidan talabijin din gwamnatin kasar Holland.

An Nuna Fim Din Batunci Ga Musulunci Tashar Talabijin Din gwamnatin Holland

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aabbir.com cewa, a jiya an nuna fin din nuna kyama da batunci ga addinin muslunci a gidan talabijin din gwamnatin kasar Holland da suna 'yancin fadar albarkacin baki.

Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da jam'iyyar nan mai tsananin adawa da musulunci take ta kara fadada ayyukanta na nuna kyama da kuma cin zarafi da batunci ga musulmi a kasar.

Gwamnatin Holland ta amince ta watsa wannan fim din ne da sunan bayar da damar fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi a tsakanin 'yan kasa.

Masu rajin kare hakkokin 'yan adam a kasar da dama sun yi tir da Allah wadai da wannan mataki da gwamnatin Holland ta bayar, na cin zarafin addinin muslunci a hukumance a kasar.

3701259

 

captcha