IQNA

An Yi Watsi Da Wata Bukatar Isra’ila Kan Iran A Zaman Majalisun Kasashen Duniya

23:06 - March 26, 2018
Lambar Labari: 3482511
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta gabatar da wata bukata a gaban taron majalisun kasashe duniya kan a yi Allawadai da Iran amma aka yi watsi da wannan daftarin kudirin.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wakilan haramtacciyar kasar Isra’ila sun gabatar da wata bukata a gaban taron majalisun kasashe duniya domin a yi Allawadai da Iran kana bin da suka kira goyon bayan ta’addanci da Iran ke yi, amma kasashen duniya sun yi watsi da wannan bukata.

A maimakon hakan ma sai aka amince da wani datarin kudiri da ke nuna goyon bayan al’ummar Palastinu da suke fuskantar zaunci da danniya da kama karya daga Isra’ila, da kuma amincewa da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Palastinu, inda wanann daftarin kudiri ya samu amincewar mutane 843 daga cikin ‘yan majalisu na kasashen duniya, wanda hakan ya mayar da shi kudiri na zaman taron.

3702051

 

captcha