Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na gwamnatin Palastine ya bayar da rahoton cewa, a cikin kwanaki biyu da suka gabata, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi fiye da dubu 40 suka kutsa kai a cikin wurare masu tsarki na musulmi a garin Khalil.
Daga cikin wuraren kuwa har da masallacin annabi Ibrahim (AS), inda suke gudanar da tarukansu na idin yahudawa, tare da keta alfarmar wannan wuri mai tsarki.
Yahudawan Sahyuniya sun hana musulmi gudanar da dukkanin ayyukan ibada a wannan masallaci mai alfarma tun daga ranar Litinin da ta gabata.
Dubban yahudawan suna keta alfarmar wannan wuri ne tare da samun kariya da daruruwan jami’an tsaron Isra’ila, kamar yadda kuma wasu daga cikin manyan sanannun malaman yahudawan Isra’ila ne suke jagorantar su.