Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, Fatou Bensouda ta bukaci manyan alkalan kotun manyan laifuka ta duniya da su bayar da dama a gudanar da bincike kan kisan kare dangin da ake zargin an yi kan 'yan kabilar Rohingya a Myanmar.
Ta ce akwai batun da ake kan cewa kasar Bangaladesh ita ce mamba a kotun ICC, amma Myanmar ba mamba ce ba, wata kila hakan ya kawo tarnaki ga duk wani bincike da za a gudanar kan hakan, ta ce a ganinta wannan ba zai saba wa ko daya daga cikin dokokin kutun duniya ba.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya da kuma masu sanya ido daga kasashen duniya daban-daban, sun bayyana kisan gillar da aka yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya a cikin kasa da shekara guda da ta gabata cewa, yunkurin share kabilar ne baki daya daga doron kasa, kuma dole ne kotun manyan laifuka ta duniya ta hukunta manyan jami'an sojin Myanmar da shugabannin addini Buda na kasar a kan hakan.