IQNA

Mai Yiwuwa Kasashen Yammacin Turai Su Kai Hari Syria

23:54 - April 11, 2018
Lambar Labari: 3482560
Bangaren kasa da kasa, a yau Jiragen yaki na kawancan da Amurka take jagoranta sun yi shawagi a kan iyakar Iraki da Syria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Amurka da kawayenta sun zargi gwamnatin Syria da yin amfani da makamai masu guba a yankin Duma da ke Ghuta da gabas.Bugu da kari Amurkan ta ce tana cikin shiri domin mai da martani akan hari da makamai masu gubar.

Tuni dai gwamnatin Syria ta karyata cewa ita ce ta yi amfani da makamai masu guban. Ita kuwa Rasha wacce ta tura masu bincike yankin ta ce babu wata alama da take nuni da an yi amfani da makamai masu guba  a yankin.

Amurka ta fara aikewa da manyan jiragen yakinta na ruwa masu dauke da jiragen sama na yaki zuba gabar ruwan Syria.

Shi kuwa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce; Nan da wasu kwanaki kadan za a dauki mataki akan harin soja a Syria.

3704849

 

 

 

 

captcha