IQNA

23:58 - April 16, 2018
Lambar Labari: 3482576

An Kame Wasu Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Zuwa Syria

Bangaren kasa da kasa, an kame wasu manyan jiragen ruwa shakare da muggan makamai zuwa Syria.

An Kame Wasu Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Zuwa Syria

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, an kame jiragen ruwan guda biyu ne dauke da muggan makamai da kuma motocin soji gami da motocin ambulance da tankokin yaki, da makaman roka da bindigogi.

An kama jiragen ne kwana daya bayan harinda Amurka ta jagoranta kan kasar, kuma an nufin mika makaman ne ga 'yan ta'adda.

Yanzu haka dai jiragen suna tsare a tasher jiragen ruwa ta Tartus dake karkashin kulawar sojojin Rasha.

3706222

 

captcha