IQNA

Dakarun Yemen Sun harba makamai masu Linzami 8 Zuwa Kudancin Saudiyya

22:52 - April 28, 2018
1
Lambar Labari: 3482613
Bangaren kasa da kasa, dakarun Yemen sun harba makamai masu linzami guda 8 zuwa Jizan da ke kudancin saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da dubban daruruwan mutane suke gudanar da janazar shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar ta Yemen Saleh Samad a yau a birnin San'a, jiragen yakin Saudiyya sun kai hare-hare a kusa da wurin da ake taron janazar, yayin da dakarun kasar gami da sojin sa kai su kuma suka mayar da martani da makamai masu linzami guda 8 a wasu sansanonin sojin Saudiyya da ke yankin Jizan a kudancin kasar.

A cikin kasa da mako guda da ya gabata, Saudiyya ta kashe fararen hula fiye da sattin a cikin kasar Yemen, daga ciki kuwa har da harin da ta kai a ranar Litinin a kan taron bikin aure, inda ta kashe mutane 33, da suka hada har da amraya, lamarin da ya fusata al'ummomin duniya da dama.

3709835

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
jika bhai Abdulrashid
0
0
Ni dai ina kira da mahakuntan saudi da su dai na aikata rashin imani akan yan shi'an yemen , in kuwa suka ki ji , to basa ki gani ba
captcha