IQNA

22:47 - May 02, 2018
Lambar Labari: 3482625
Bangaren kasa da kasa, dakarun yahudawan sahyuniya sun kai wani samame a yankin Kilkiliya a yau da rana tsaka a kan al'ummar Palastine mazauna yankin.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kafofin yada yada labaran Palestine sun bayar da rahotanni da ke cewa,a  yau da ran atsaka jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila da suka hada da sojoji da kuma 'yan sanda, sun kutsa kai a cikin garin Kilkiliya, inda suka rufe babbar mashigar garin.

Bayan shigar su sun yi ta bincike a cikin gidajen palastinawa mazauna garin, kamar yadda kuma suka kame wasu matasa suka yi awon gaba da su.

Haka nan kuma sun yi ta antaya hayaki mai sanya ahawayea  ko'ina a cikin unguwanni, lamarin da ya sanya mata da kanan yara suka yi shakewa, kamar yadda kuma suka yi ta tarwatsa yara a lokacin da suke tashi daga makarantunsu.

3711124

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: