Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin haihuwa Imam Mahdi (AJ) an gudanar da irin wannan taron a birnin Moscow na Rasha.
Daruruwan masoya iyalan gidan manzon Allah ne dai suka tarua wurin taron, inda aka gabatar da jawabai.
Bayanin ya ci gaba da cewa Fathi daya daga cikin malaman jami'ar Imam Sadeq (AS) ya gabatar da jawabia wurin.
Bayan sa kuma Hojjatol Islam Akbar Jiddi shi ma daya daga cikin malamai da suka halarci ya gabatar da jawabi kan matsayin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Alalh ya tabbata agare shi da alayensa.