IQNA

23:47 - May 24, 2018
Lambar Labari: 3482690
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar ilimi ta lardin Qana a kasar Masar ta girmama mahardatan da suka fi nuna kwazo a gasar kur’ani ta lardin.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, an girmama mahardata 39 daga cikin wadanda suka halrci gasar kuma suka fi nuna kwazo a dukkanin bangarorin da aka gudanar da gasar a kansu.

Rahoton wadannan dalibai da suka samu wannan girmama a tsakanin mahalarta gasar su 1200 sun taka rawar gani matuka a gasar.

Wannan gasar kur’ani da aka kammala jiya alhamis a lardin Qana na Masar, ta kunshi daliban makarantun sakandare ne kawai, kuma a kan gudanar da gasar ne a cikin kowane watan Ramadan mai alfarma.

3717202

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: