IQNA

22:12 - May 26, 2018
Lambar Labari: 3482696
Bangaren kasa da kasa, an bude babbar gasar kur’ani mai sarki karo na ashirin da bakawai a kasar Libya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na libyaakhbar.com ya bada rahoton cewa, a jiya an bude babbar gasar kur’ani mai sarki ta kasa baki daya karo na ashirin da bakawai a Libya a birnin Baida.

Bayanin ya ci gaba da cewa an dauki tsawon shekaru ashirin da bakwai a jere ana gudanar da wannan gasa, wadda take samun halartar daruruwan makaranta da mahadata kur’ani mai tsarki daga dukkanin sassan kasar.

A wannan karon ma gasar ta samu halartar makaranta da mahardata daga wasu sassan kasar, amma wasu sassan kasar ba su samu halata ba, sakamakon irin halin da kasar tak ciki.

Matamakin frayi ministan kasar ne da ya jagoranci bude taron gasar, gami da jami’ai daga ma’aikatar ilimi da kumama’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

3717557

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: