Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai an sadal balad ya bayar da rahoton cewa, Khalid Mahmud Hijaz da ‘yar uwarsa Khalud, dukkaninsu ‘yan shekaru 13 ne, kuma an haife su ne a garin Ishaqa da ke cikin gundumar Kafar sheikh a kasar Masar.
Dukkanin matasan biyu dai makafi ne, amma Allah madaukakin sarki ya albarkac rayuwarsu da hardar kur’ani mai tsarki.
Khalid ya bayyana cewa, tun suna aji na uku a firamare suka fara harda, amma saboda matsaloli da rashin kayan aiki da za su taimaka musu a makaranta, ba su samu damar ci gaban hardar ba.
Amma daga bisani bisa taimakon iyayensu da kuma babban dakin karatu na garinsu, sun samu irin kayan da suke bukata da za su taimaka musu wurin hardar kur’ani mai tsarki.
Yanzu haka suna halartar darussa a makaranta, kuma suna ci gaba da kokari a bangaren hardar da suke yi.